Littafin Farko babin bayanin hukuncin ruwa
Babi Na Farko Shine Hukuncin Ruwa Mai Tsarki
1. An kar~o daga Abi Huraira Allah Ya yarda dashi yace: ‚Manzon Allah (S.A.W) yace ‚A game da ruwa kogi: ‚Ruwansa mai tsarki ne, kuma mataccensa halatacce ne.‛ Mutane hu]u suka ruwaito, da ]an Shaiban kuma lafzinsane kuma ]an Khuzaima ya ingantashi da shi da Tirmizi (kuma Malik da Shafi’u da Ahmad suka ruwaitoshi.‛ (Hadisin Isnadinsa Ingantacce ne).‛ 2. An kar~o daga Abi Sa’idul Khudiri Allah Ya yarda da shi yace: ‚Manzon Allah (S.A.W) yace: ‚Lallai ruwa mai tsarkine, wani abu baya sashi ya zama najasa da komi.‛ Mutane uku suka ruwaito shi, Kuma Ahma ya inganta shi. (Hadisin Ingantacce ne).‛
3. An kar~o daga Abu Umamata Al-bahili Allah Ya yarda da shi yace: ‚Manzon Allah (S.A.W) yace: ‚Lallai ruwa baya najasa da komi sai abinda ya ~ata warinsa da ]an]aninsa da launinsa.‛ (Ibn Majah ya ruwaito shi.‛ ‚Amma Abu Hatim ya raunana hadisin. (Hadisin Dwa’ifi ne).‛ An kar~o daga Baiha}i cewa: ‚Ruwa mai tsarki ne, sai dai abinda ya canza wurinsa, da ]an]aninsa, da launinsa, da najansa wanda ya faru a cikin sa.‛
4. An kar~o daga Abdullahi ]an Umar Allah Ya yarda da su yace: ‚Manzon Allah (S.A.W) yace: ‚Idan Ruwa ya kasance a cikin tulu biyu to ba zai ]auki najansa ba.‛ A cikin wani lafazi ‚Bai sashi najasa.‛ Mutane hu]u suka ruwaito.‛ Kuma ]an Khuzaima ya ingantashi, da shi da Hakim da ]an Hibban.‛ (Hadisin Ingantacce ne).‛
5. An kar~o daga Abi Huraira Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Manzo Allah (S.A.W) ya ce: ‚Kada ]ayanku yayi wanka cikin ruwan da ya ke wuri guda baya gudu Alhali yana da Janaba.‛ Muslim ya ruwaito.
6. Daga Bukhari Ruwaito shi cewa: ‚Kada ]ayanku yayi fitsari a cikin ruwan da yake dawwamamme (wanda baya gudu) sa’an nan ya yi wanka a cikinsa.‛ An kar~o daga Muslim cewa: ‚Sa’an nan ya yi wanka daga gare shi.‛Daga Abi Dawuda cewa: ‚kada yayi wanka cikinsa na janaba.
7. An kar~o daga wani mutum Sahabin Annabi Allah (S.A.W) ya ce: ‚Manzon Allah (S.A.W) ya hana mace tayi wanka da sauran ruwan wankan mijinta, ko na miji ya yi wanka da sauran ruwa mace, Sai In da su kaffata gaba ]ayan su.‛ (A cikin lokaci Guda) Abu Dauda ya ruwaito da Nisa’i suka fitar da shi. Kuma Isnadinsa Ingantacce ne. (Hadisin Ingantacce ne).‛
8. An kar~o daga ]an Abbas Allah Ya yarsa dashi cewa: ‚Lallai Annabi (S.A.W) ya kasance yana wanka da sauran ruwan wankan Maimuna.‛ Muslim ya ruwaito.
9. An kar~o daga sahaban Sunan cewa: ‚Daga sashen Matan Annabi (S.A.W) tayi wanka a cikin wata kwatanniya, sai yazo zai yi wanka daga gare ta, sai tace masa ni na kasance ina da janaba, (watau, wankan janaba nayi) sai yace: ‚Lallai ruwa janaba baya samunsa.‛ Tirmizi da ]an Khuzaima suka inganta shi.
10. An kar~o daga Abi Huraira Allah Ya yarda dashi yace: ‚Manzon Allah (S.A.W) yace: ‚Tsarkin }waryan ]ayanku idan kare yayi lallaga cikinsa, to, ya wanke shi sau bakwai, na
8
farkonsu da }asa‛. Muslim ya ruwaito: ‚Amma a ciki wani lafazin nasa. To, ya zubar da shi‛. Kuma a cikin ruwayan Tirmizi cewa: ‚Ta }arshensu ko ta farkonsu (Wato wankin }waryan da }asa)‛.
11. An kar~o daga Abi {atada Allah Ya yarda dashi ya ce: ‚Lallai Manzon Allah (S.A.W) yace: ‚Geme da Hukuncin kyanwa (wato mage) ‚Lallai ita ba najasa ba ce. Amma dai ita kawai ta zama tana zagawa ne tsakanin ku.‛ Kuma mutane hu]u suka ruwaito shi‛. Kuma Tirmizi da ]an Khuzaima suka Inganta shi.‛ (Hadisin Ingantacce ne)‛.
12. An kar~o daga Anas ]an Malik, Allah Ya yarda da shi ya ce: ‚Wani Balarabe yazo, sai ya yi fitsari cikin Haraban masallaci, sai mutane suka yi masa tsawa, sai Annabi (S.A.W) ya hanesu.kuma daga bayan ya gama. Sai Annabi (S.A.W) yayi umurni a akawo cikin guga na ruwa aka zuba akansa‛. (wato fitsarin) Bukhari da Muslim suka ruwaito.
13. An kar~o daga ]an Umar Allah Ya yarda da shi, ya ce: ‚Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ‚An halatta mana matattu biyu, da jinni iri biyu. amma kuma matattu biyu, sune fara, da kuma kifi, da kuma jini biyu, sune hanta, da kuma }oda‛. Ahmd ne da ]an Majah suka ruwaito shi‛. Amma a cikin hadisin akwai rauni‛. (Hadisin Albani ne ya Inganta shi)‛.
14. An kar~o daga Abi Huraira Allah Ya yarsa da shi ya ce: ‚Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ‚Idan }uda ya fada a cikin abin shanku to ya tsomashi cikin sanan ya cire domin kuwa daya fikafikinsa cutane daya kuma magani; Bukhari ya ruwaito da Abu Dauda sanan ya kara da cewa shi ana wanke wane daga fikafiki mai cuta.
15. An kar~o daga Abi Wa}idil Laisi Allah Ya yarda da shi yace: ‚Annabi (S.A.W) ya ce: ‚Duk abin da aka ciro daga dabba yana raye to mushene. Abu Dauda da Tirmizi suka ruwaito kuma suka kyautatashi. Kuma lafazin sane.‛ (Hadisin Ingantacce ne).‛

Post a Comment
0 Comments